- Kaduna Press
©29/1/2022
 27/6/1443H

A yau A 29/1/2022 dai dai da 27/6/1443, da misalin karfe goma (10:00am) na safe Sisters forum Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H), na garin kaduna sun gudanar khatamar maulidin yar Manzon Allah (S) Sayyid Fatima Az-Zahra (S.A) an gudanar da wanna taro ne a hayin Rigasa Kaduna.
Bayan bude taro da Addu'ah da karatun Alqur'ni, sai ka shiga filin mawaka, sannan a ka karanta Ziyarar ga Sayyid (S.A), Faretin girmamawa gareta.

Sai kuma a ka gabar da mai jawabi Sharif Musa Musaddiq a cikin jawabin sa Malam ya kawo wani Hadisi da ya ke cewa: Fatima ta kasance mai dauke da ruhin Manzon Allah (s.a.w.a) da dabi'unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama da shi, sannan ya kara da cewa: "Fatima wani yanki ne na jikin Annabi (S). Sannan shugabar matan duniya". 
Sayyida ta kasance tana ji da mahaifinta (S) da tausaya masa irin tausayin uwa ga 'ya'yanta, tana kuma lura da shi kamar yadda uwa ke lura da 'ya'yanta, hakan ya sa Manzo Allah (S) ya kirata da Mahaifiyar Babanta (Ummu Abiha). Malam ya kawo falala da darajojin Sayyida Fatima (S.A), so sai.
A ka mika a bun magana ka wakilin Almajiran Sayyid Zakzaki na garin Kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizi) in da ya gabatar da gajeren Ta'alik. Malam ya fara ne da mika godiya ga Allah, da ya kawo mu karshen taro (Khatama) na wanna  shekara lafiya,  Sannan malam ya yi kira ga mahalarta taron da su fahimci, girman Sayyida Fatima (SA) don daukar darasi daga rayuwarta, sannan ya kara da cewa: karda ka/ki sake a yi mauludi a tashi ba ka dauki abin koyi daga rayuwar Sayyida ba.
Sannan Malam yayi kira ga Almajiran Sayyid Zakzaky na grain Kaduna da su daure su ba da gudumuwa mai tsoka a maulidin Imam Ali da za a fara gudarwa, nan da mako mai zuwa.

Haka shima Pastor Yohana Y Buru Shi ma ya fara ne da yiwa Allah godiya da wannan gayyata da ya samu, sannan yayi Addu'a ga jagoran Harkar Musulunci Sayyid Ibrahim Zakzaky, sannan yayi kira da a kara cigaba da hadin kai, yace masu iya magana na cewa: (a hankali a hankali matankadi ke shiga bakin gora) dan haka a cigaba da hadin kai da sannu za a cimma buri, bisa ga imanin mu, sannan ya yi kira ga sisters da suyi koyi da yar Manzon Allah, a karshe Pastor yayi addu'ah Allah ya hada kan Al'umar Kasan nan, Musulmi da Kista, da ma wanda bai da addini.

Sannan a ka mika abun magana ga shugaban Sisters forum na garin Kaduna Malam Jamila Auwal ( Muktar Sahabi Kaduna) in da ta jawo hankalin Sisters da su lazzama wa kansu wani rayuwa da ga cikin rayuwar Sayyida, tsakanin su da Allah, karda ya zama suna rayuwa na al'ada, basu da hadafi, sannan kowacce ta kalli kanta daga mauludodin bara zuwa yau kin cenza? Ko kuwa baya kikaci?
Daga karshe an Bayar da lambar yabo ga Halkokin da suka fi bajinta a wannan shekara 2022-1443H, Halkar Imam Mahdi (As) ta zo na daya (1) Sai Halkar Imam Hassan (As) tazo na biyu (2) Sai na uku Halkar Imam Hussain (As) (3) sannan ka raba takardan shaida (Certificate) da yabo da dukkan Halkoki, a ka gabatar da walima, a ka raba kyaututtuka a ka yi addu'ah, ka sallami kowa.

- Kaduna Press
©29/1/2022
 27/6/1443H