Mabaruka Abdullahi✍️
KD-PRESS🌐
©30/6/2023

Cutar sanqaron mama (breast cancer) Cutar sanqaron mama cutace datake latata fata, kwayoyin halitta, da duk wani sassar dake jikin mama wanda yaka janyo ciwo a jikin fatan maman dama maman baki daya
    
IRE-IREN CUTAR

Cutar sanqaron mama ya kasu kashi biyu
1.akwai wadda take yaduwa (inversive)daga kan fatan maman zuwa cikin maman kuma shine mafi tsanani shi kuma akafi sani saboda shi akafiyi
2. Akwai kuma non inversive wanda shine yake taimakawa inversive din wajen yaduwa a jikin fatan maman dama duka sassan maman
            
         ALAMOMIN CUTAR

1.zafi daga kan maman
2.kurzunu-kurzunu ajikin maman
3.zubar ruwa daga kan maman
4.canzawar kalar fatan maman
5.yaqunewa/kankancewar kan maman
6. Wani lokacin hannu daya yana kumbura(hannun dake bangaren da cutar ya fara)
 
             ILLOLIN CUTAR
Cutar sanqaron mama tanada illoli dayawa amma wanda tafi hatsari shine ba,a iya ganeta da wuri, wani lokacin takan dauki tsawon shekara ajikin mace batareda tasan tanada itaba.
Sannan idan ya kasance a danginku ko agidanku wani tanada ita to kuma kuma ita kasancewa at risk na kamuwa da cutar.

HANYOYIN DA ZA,ABI WAJEN KARE KAI DAGA KAMUWA DA CUTAR

1.yawan screening da kanki domin tabbatar da bawani abu daya canza ajikin mama
2.ki tabbatar ba wani kurzunu-kurzunu a jikin maman
3.cin abinda zakara wa maman lafiya
4.shan katana marmari akai akia
5.cin abinci mai kyau
6.sannan a sings yawan ziyartar kwararrun likitoci  domin tabbatar da lafiyarki