a wani samame da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan kafin asubahi, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA, wanda ya ambato majiyoyi da dama.
Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19 a wani samame da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan kafin asubahi, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA, wanda ya ambato majiyoyi da dama.
Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa biyu waɗanda suka dawo daga aikin Hajji a kan iyaka da Jordan, in ji WAFA. An sace sauran mutanen ne a garuruwan Tulkarm, Nablus, Yatma, da Ramallah.
An sace mutanen ne ba tare da wani sammaci ba, kuma dakarun Isra'ila sukan yi irin wannan garkuwa da Falasɗinawa a duk inda Isra'ila ta ga damar yin amfani da ƙarfin-tuwo don cin zarafin Falasɗinawa.
Sojojin Isra'ila sun sace tare da ɗaure Falasɗinawa sama da 9,500 tun daga watan Oktoban da ya gabata, idan aka kwatanta da Isra'ilawa 116 da Hamas da sauran ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa suke tsare da su a Gaza tun wancan lokacin.
0 Comments