Imam Hassan (AS) shi ne limami na 2 daga cikin limaman Ahlul bait (AS) 12 An haifi Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) ne ranar sha biyar ga watan Ramalana mai albarka shekara ta uku bayan hijira. Mahaifansa kuwa su ne tsarkakan halittun nan guda biyu wato: Imam Ali da Kuma Fatima al-Zahra (a.s).
Haihuwarsa ke dawuya sai aka sanar da Manzon Allah al-Mustafa (SAWA) da kuma albishir saboda wannan karuwa da aka yi, shi kuma sai ya garzaya gidan Fatima (AS) don taya murna da farin nuna farin cikinsa.
Koda isowarsa sai aka gabatar masa da wannan jariri mai albarka, Manzo ya karbe shi da hannayensa mai daraja, ya sumbace shi, ya rungume shi a kirjin sa; sai ya kira sallah a kunnensa na dama, ya yi ikama a na hagu, don sautin gaskiya ya zama farkon sautin da ya fara ratsa samuwarsa da jinsa. Sai Manzo (SAWA) ya waiwayi Ali (AS) ya ce: "Wane suna ka sa ma dana?" sai Imam Ali (AS) ya ce: "Ban kasance mai shiga gabanka ba ." sai Manzo ya ce: "Kamar yadda nima ban kasance mai shiga gaban Ubangijina ba." (Wato ma'ana ni ma ba zan gabaci Ubangiji wajen sa masa suna ba. Wannan tataunawa ba ta kai gacinta ba sai ga Wahayin Allah na saukowa ga Manzon Allah (SAWA) , wanda ke sanar da shi cewa Allah Madaukaki Ya sanyawa abin haihuwa suna Hassan.
Lokacin da kwanaki bakwai da haihuwa suka kewayo, sai Manzo (SAWA) ya yanka masa rago na radin suna, daga ciki ya ba unguwar -zoman da ta karvi haihuwarsa cinya tare da dinari daya, wannan a matsayin godiya bisa kokarinta a madadin abin haihuwa da mahaifiyarsa mai tsarki. Sannan ya kama kan abin haihuwa ya aske, ya yi sadaka da nauyin gashin shi da azurfa wanda ya yayyafe shi da wani nau'in turare da ake kira da Khaluq; sannan ya sa aka yi masa kaciya.
KD-PRESS
©25/3/2024
15/Ramadan/1445
0 Comments