KD-PRESS✍️
A yau Litinin 25/3/2024 Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na da'irar Kaduna sun gudanar da Taron Tunawa da ranar zagayowar haihuwar Imam Hassan almujtaba limami na biyu daga cikin limaman sha biyu daga cikin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa. Taron ya gudana ne da misalin karfe uku da rabi (3:30pm) na yamma a muhallin fudiyya dan Madami Rigasa Kaduna.
An bude taron ne  da Addu'ah, sai aka gabatar da karatun Alkur'ani Mai girma, Sai filin mawaka inda suka gabatar da wake murnar haihuwar Imam Hasan (As).

Bayan sun kammala sai aka gabatar da babban bako mai Jawabi, Shaikh Abdul Malik in da ya gabatar da Jawabi dangane da Imam Hasan Almujtaba (As). Malamin ya yi gamsasshen Jawabi, inda ya fado falaloli da martabobi na Imam Hasan (As). Bayan haka Malam Aliyu Umar Tirmizy ya gabatar da Ta'aliki dangane da Jawabin, shi ma ya yi karin haske sosai ga mahalarta Taron, daga bisani ya tabo bangaren Malam Mukhtar Sahabi, yayin da ya tabo bangarori daban daban na rayuwarshi.

Bayan haka, Sistoci (Sisters Forum) na Kaduna sun bayar da tallafin kayan abinci ga iyalan wadanda su ka rasu.

Daga karshe an yanka alkaki sannan aka raba walima, anyi taron  lafiya kuma an kammala lafiya,

Ga wasu hotuna da mu ka dauko maku a wurin .

KADUNA PRESS✍️
©15/09/1445
25/03/2024