Ummul Muminina Khadijah bint Khuwailid, matar Ma'aikin Allah (s) ta rasu ne a ran 10 ga watan Ramadan shekara ta goma da aiko Ma'aiki (s), wato shekara uku kenan kafin hijira, a lokacin kuwa tana da shekaru 65 a duniya.
Kafin rasuwarta dai, Khadijah ta ba da gudummawa mai girman gaske wajen kare Ma'aikin Allah (s) da kuma ci gabantar da Musulunci a lokacin da yake cikin mawuyacin hali. Saboda irin wannan gagarumar gudummawa da Nana Khadijan ta bayar ne aka ruwaito Manzon Allah (s) yana cewa: 'Ba don kariya ta Abu Talib ba, da kuma dukiyar Khadijah da kuma takobin Ali ba, da wannan addini bai tsaya ba da kafarsa ba.
Wannan rasuwa ta Khadijah dai ya kasance babban rashi ga Ma'aikin Allah da kuma 'yarsa Fatima (a.s) inda har tazo tana kuka tana ce Baban nata (s) ina mahaifiyata, nan take sai Mala'ika Jibril (a.s) ya sauko ya ce wa Annabi (s): "Ka ce wa Fatima cewa Allah Madaukakin Sarki Ya gina wa mahaifiyarta gida a aljanna da zinare....".
Hakan kuma saboda irin wannan babban musiba da ta sami Manzon Allah (s) na wannan rashi na Khadijah da kuma rasuwar baffansa kuma mai kare shi Abu Talib (a.s), ya sa ya kira wannan shekara (da suka rasu a cikinta) da "Shekarar Bakin Ciki".
Kaduna Press
©11/4/2022
Muna Yiwa Dukkan Al'ummar Musulmi Jaje Na Rashin Uwar Mumunai Nana Khadija (SA).
0 Comments