A Yau Talata 11/1/2022 Sister forum Almairan Sayyid Zakzaky (H), Na Halkar Imam Hussain Kaduna (As) sun Gudanar da Mauludin Sayyida Zahara (SA), a kurmin Mashi,
An fara taron ne da Addu'ah  
Sai karatun Alqu'rani mai girma, maraba da baki, ziyaran Sayyida Zahara (SA),
Sannan a ka Gudanar da Faretin Girmamawa ga Sayyida, Sai aka gabatar da mai jawabi.
Mai jawabi ta farko Mallama Khadija Hassan (Maman ambato) Kaduna 
Tagabatar da jawabi a kan rayuwan Sayyida Zahara sanan ta tabo wasu janibobi da dama, inda mallaman take  cewa duk wani abun da a ke nima na tarbiya to za a sameshi ne acikin rayuwan sayyidah Zahara.
Sanan tace duk hidiman da uwa kema danta to shi sayyidah Zahara takema Abbanta, mace ce mai hidimtama gidanta baki daya, bawai sai tajira daga mijinta ba.
Fanin kiwon lfy kuwa Tana da ilimi na likitance . Sanan Tana da ilimin tarbiyartar da yara, domin a ka'ida ya kamata kafin yaro yafara zuwa makaranta to ya ra samun ilimin farko daga mahaifiyya.
Wannan a bun koyin yakamata mukoya wajan bawa yara ilimi tundaga gidajen mu.
Itakuwa Mallama Lubabatu Alhassan Rigasa, tayi ta'aliki, Inda take cewa: Sayyidah Zahara, ta tsara rayuwanta ne dai dai da hidiman mijinta, Bata tambayansa abun da bashi dashi. Wanan babban a bun koyi ne, ga masu aure, Yazama wajibi ga masu bin Ahlu-lbayt suyi koyi da rayuwan Sayyidah Zahara. Tun daga kan ibadanta har zuwa hakurinta dama sadakanta. 
Tana Sallah ne tunfarkon dare harzuwa goshin Asuba. Sannan ta kara kira ga mahalarta taron da su zama masu ibada da kyauta kada su zama masu rowa sanan su zama masu kamewa.
Hadisi yazo cewa: duk Wanda yake kyakkyawan aiki to yafi aikin kyau a wajan Allah, haka nan duk mai mummuna  aiki to yafi aikin muni a wajan Allah.

Sannan a ka mika abin magana ga wakilin Almajiran Sayyid Zakzaky na garin Kaduna, Sheikh Aliyu Umar (Tirmizi) in da ya yi 

Shikuwa mallam aliyu tirmi kaduna inda yayi Ishara ga masu wullayah ga Ahlul-Bayt (As) yace: duk mabiyin Ahlul-bayt Yazama dole yafikowa  dabi'a mai kyau.
Daga karshe an yanka alkaki, a ka raba walima da kyaututtuka, a ka gabatar da jawabin godiya a ka sallami kowa.
Ga Wasu Daga Cikin Hotunan Da Muka Dauko Muku A Wajan.

Kaduna press
11/1/2022