Batoul K/mashi
KD-PRESS 🌐
©6/6/2024
lunguna, sai muka bullo bakin hanya muka (sallaka titi, mukag angara wani dan lungu, sai ga mu a gidan. Bayan an gaggaisa, Ayya ta ce, "Halima ga 'yarki na kawo miki." Halima ta ce. "Allah ya taya ni riko." Ayya ta dauko kudi ta mika min ta ce. "kudinki ne lokacin da kika shiga Musulunci aka tara miki. Na yi godiya dauki dari biyu na ba ta ta ki karba.
Malam Yahaya Kirfi koyarwa yake yi a Federal Polytechnic Bauchi. Yana da mata biyu, Uwargidan sunanta Halima: yaran gidan suna kiran ta da Umma. Amaryar kuma sunanta Hafsat, yaran gidan na kiran ta da Yadikko. Umma' ya'yanta uku. tana dauke da cikin na hudu. Ya'yan sune Sajida. Siddika, Salma.
yayin da ita kuma Amaryar 'ya'yanta biyu: Sabira da Salim. wacce ake goyo. Sai kanin Maigidan mai suna Tajo.
Ran Lahadi bayan mun ci abincin dare. sai mun zauna muna dan hira muna kallon talabijin. Can sai aka fara gabatar da labaran karfe tara na N.T.A Abuja. Fatima Abbas ce take gabatar da labaran. Na natsu ina sauraron matar saboda tana burge ni sosai.
Bayan ta gama labaran ne aka ci gaba da watso shirin nan na Newsline. Kwatsam aka nuno hotona baro-baro a cike da talabijin da sanarwa kamar haka cikin harshen Turanci:
Cigiya! Cigiya!! Cigiya!!! Ana cigiyar Chinyere wadda ta
bace a garin Jos ran daya ga watan Agusta, dalilin motarsu ta tsaya domin cin abinci. Chinyere 'yar shekara sha bakwai da haihuwa fara ce mai matsakaicin tsawo. Tana da 'yar kiba kadan tana sanye ne da doguwar riga launin rawaya mai adon 'yan duwatsu a gaban
rigar: kuma tana sanye da bakar hula na sakakken bakin lilo. Ana rokon jama'a duk wanda Allah ya sa ya gan ta ya sanar da ita cewavyayenta suna neman ta da gaggawa, ko a sanar da Hukuma mafi kusa. Sanarwa daga Mista Chibuzor da iyalansa.
Muka yi shiru muna sauraron sanarwar da ke fita daga cikina kwatin talabijin. Umma ta nisa, "Fadima kin ji iyayenki sunan eman ki." Kafin in amsa Malam ya yi sallama hannusa rike da buta, "sanarwar me nake ji daga bayan gida?" Umma ta labarta masa kamar yadda muka ji, yayin da gaba dayanmu hankulamlnmu suka tashi. Malam yace: ba komai Halima ki kula sosai ban da aikenta ko ina iyakar ta cikin gida.
Shiga nan Dan cigaban labarin👇🏼
```Wanna Labari Zai Dunga Zuwa Muku Duk Ranar Alhamis Da Juma'a```
_Kubiyo Mu A Rubutu Nagaba Dan Jin Cigaba_ ...
Batoul K/mashi
*KD-PRESS* 🌐
©6/6/2024
0 Comments