Wata ƙungiya mai fafutuka a Moroko ta buƙaci gwamnatin ƙasar da ta gaggauta dakatar da wani jirgin ruwa na dakon kaya 'Vertom Odette' da ake zargin ya dauko makaman Indiya zuwa Isra'ila daga wucewa ta yankin ruwanta.

Jirgin ruwan wanda ya baza tutar ƙasar Luxembourg ya taso ne daga Indiya a ranar 18 ga watan Afrilu kuma ana sa ran isarsa tashar jiragen ruwa ta Cartegena a ranar Laraba, kamar yadda kafafen yada labarai na Maroko suka rawaito ƙungiyar Moroccan Front da ke tallafa wa Falasdinu tare da adawa da abubuwan da ke faruwa a ƙasar ta bayyana.

Idan za a shiga ta Tekun Bahar Rum, dole sai jiragen da ke tafiya yankin gabas daga Tekun Atlantika sun bi ta Mashigar Gibraltar, wanda ya raba ƙasar Spain da Maroko.

A wata wasiƙa da ta aika wa gwamnatin ƙasar, ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan cewa ana zargin jirgin da jigilar kayan yaki ne da zai kai zuwa Isra'ila, kazalika ta bukaci gwamnatin da ta gaggauta daukar mataki don gudun abin da ka iya zuwa ya dawo na zargin Moroko da hannu a ''laifukan yaƙi.''

''Manufar wannan wasiƙa ita ce janyo hankalin gwamnati don ta dakile duk wani zargin hada baki da Maroko wajen aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a idon duniya da dokokin kasashen duniya,'' in ji ƙungiyar.

Kazalika wasiƙar kungiyar ta kara da cewa: ''hukuncin da Kotun Duniya ta yanke na baya-bayan nan ya bayyana cewa dole Isra'ila ta yi taka tsan-tsan wajen aikata kowane irin laifi da ya shafi kisan kare dangi kan Falasdinawa.

"Wannan mataki zai sanya zargin hannu a kisan kare dangi kan duk wata gwamnati da ta taka rawa wajen sauƙaƙa hanyar samar wa Isra'ila makamai cikin sauki ."

Yakin kisan kare dangi

A bangare guda, darurwan mutane ta shafukan intanet sun yi ta ƙira ga hukumomi da su ɗauki dakkan matakan sa suka dace wajen hana jirgin ruwan Vertom Odette wucewa ta hanyar ruwan Maroko tare da tabbatar da cewa bai isa zuwa Isra'ila ba.

Kasashen duniya da dama sun yi ta zanga-zangar nuna adawa da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Tun daga watan Oktoba shekarar 2023, Isra'ila take ta kai munanan hare-hare a Gaza duk da wani kuduri na kwamitin sulhu na MDD da ya bukaci a gaggauta tsagaita wuta.

Tel Aviv ta kashe Falasdinawa sama da 36,500, galibi mata da kananan yara tare da raunata kusan mutum 83,000, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

Kusan watanni takwas kenan da yaƙin Isra'ila, yankunan Gaza sun zama kango a yayin da aka hana shiga da abinci da ruwa mai tsafta da kuma magunguna.

Ana tuhumar Isra'ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya, wadda a hukuncin da ta yanke na baya-bayan nan ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da kai hare-hare a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka.