Masu fallasa bayanan sirri na Isra'ila sun bayyana wani yanayi mai tayar da hankali a sansanin hamadar Sde Teiman, wani sansanin soji da ya zama cibiyar azabtarwa a cikin hamadar Negev, a cewar wani rahoto daga CNN.

Falasɗinawan da ake tsare da su a wajen waɗanda Isra'ila ta kama ne a lokacin da ta kutsa yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya.

Masu fallasar, waɗanda ke fuskantar hukuncin shari'a da kuma ramuwar gayya daga ƙungiyoyin da ke goyon bayan munanan manufofin Isra'ila a Gaza, sun bayyana cewa fursunonin da ake tsare da su na cikin matsanancin yanayi da kuma ɗimauta.

"An ga jerin mutane sanye da tufafi masu launin toka suna zaune a kan katifu 'yan shafal-shafal, an zagaye su da waya, dukkansu an rufe idanuwansu da ƙyallaye an rataye kawunansu a ƙarƙashin hasken fitulu," in ji rahoton, yayin da yake ambato masu fallasar.

"An gaya mana cewa ba a yarda su dinga motsi ba. Sai dai su tsaya a yanayi guda ƙyam. Ba a yarda su yi magana ko su dinga leƙe daga cikin mayanin da aka rufe musu idanuwa ba.

'Ramuwar gayya'

Rahoton ya ce "fursunonin suna cikin matsanancin yanayi, sannan wasun su an ajiye su a wani ɗakin mai kamar na asibitin inda aka ɗaure fursunonin da suka ji rauni a jikin gadajensu, an sanya musu ƙunzugun zamani wato famfas, kuma ta cikin wani ɗan kwaroron roba ake ba su abinci."

Wani mai fallasa, wanda ke aiki a matsayin likita a asibitin, ya ce: "Sun cire musu duk wani abu da ya yi kama da mutane."

An lura cewa an umurci masu gadi da su rufe bakin fursunonin kuma su ware “masu ba da matsala” don hukunta su.

Wani mai fallasar ya ce ana kuma dukan mutanen, ba da zummar samun bayanan sirri a bakinsu ba sai don "ramuwar gayya."

Bayanan masu fallasar sun kuma nuna damuwa a kan yanayin kula da lafiya a sansanin.

Wani kuma ya sake cewa "akwai waɗanda aka yanke wa wasu gaɓɓan jiki saboda yawan raunukan da suka samu sakamakon yawan ɗaure musu hannaye ko ƙafafu da ankwa; kuma ana yanke gaɓɓan ne ta hanyar tiyata da wasu likitocin da ba ƙwararru ba ke musu," ya ƙara da cewa.

Da take mayar da martani kan rahoton na CNN, rundunar sojin Isra'ilan ta ce ana bibiya da ɗaukar matakan da suka dace a kan duk wasu zarge-zarge.