Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa kasashen yamma suna son cusa gaba tsakanin kasarsa da China wanda ya kasance daya ne daga cikin yakin farfaganda kan kasarsa daga wadannan kasashe.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Lavrov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da ‘I Fakty News’ na shafin yanar gizo wanda kuma aka yada a yau Talata.
Lavrov ya kara da cewa kasashen yamma suna cewa dangantakan Rasha da China ba dangantaka ne na kasashe wadanda suke matsayi guda ba, wai ba za’a kwatanta China da Rasha ba.
Sana ganin Rasha ce take bukatar karfafa dangantaka da China ba akasin haka ba.
Saboda kasar Rasha tana cikin matsaloli da dama wadanda suka hada da yakin da take fafatawa da Ukraine a halin yanzu.
Ministan ya bayyana cewa makiyan kasashen biyu ne suke fadar haka tun da jimawa, saboda basa son ganin irin yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake kara habaka.
Tun shekara ta 2022 ne dangantaka tsakanin kasashen biyu ya fara bunkasa tsakanin Begin da Mosco. Sannan abokantakan kasashen biyu ya kai ga shugaba Xi na kasar China yace babu iyaka a dangantaka tsakanin kasashen biyu.
0 Comments