A yau Alhamis 6/1/2022 da misalin karfe uku na rana (3:00pm) Almajiran Sayyid Zakzaky na Da'irar Kaduna suka gudanar da tunawa da shahadar yar fiyayyan halitta Annabi Muhammad (s.a.w).
Bayan bude taro da addu'a da karatun Qur'ani sai Majlisin juyayi yabiyo baya, bayan tamsiliyya da karanta ziyarar yar Fiyayyar halittar (a), sai jawabi ya biyo daga baya daga bakin wakilin Almajiran Sayyid Zakzaky na Da'irar Kaduna Sheikh Aliyu Umar ( Tirmizi), Malam yafara karanta jarabawowin da Sayyida din ta fuskanta tun tana yar shekara biyu, ya karanto zantukanta dake nuna yanayin tsananin rayuwar da ta fuskanta tun ranar da aka binne Babanta Manzon tsira (S), inda take wasu baituka tana me cewa; "An tunkudomun musibun da da za a tunkudowa yinnai sai sun zama darare".
Ya ci gaba da karanto musibun da ta fuskanta har takai ga mutanen madina suna cewa; a je agayawa Ali (As) ya cewa Azzahra (As) ta za6i lokacin kuka ko dai tarinka kuka da daddare ta barmu muyi bacci da rana, ko tayi kuka da rana ta barmu muyi bacci da daddare, daga karshe ta za6i a gina mata Gida a wajen gari, kuma Ali (a) yabi Umurninta ya Gina mata Gida ko Daki da ake kira da Baitul Huzun.
Har takai daga karshe an samu wasu dake qaddara mabiya mahaifinta ne sukaje har Gida suka buge kofar gidan tana bayan kofar suka buge kofar tafadi kasa, dalilin da yasa tayi 6arin cikin dan da take dauke da shi me suna Muhsin.
Daga karshe a wannan yanayi na kunci da rashin walwala da suka cika rayuwar ta, ta koma ga Allah tana matsayin wacce aka zalunta, abinda ke tabbatar da hakan shine fadinta daya shahara; " Ya Ali! Kada kabari wadanda suka cutar dani su halarci jana'izata".
Amincin Allah ya tabbata agareki ranar da aka haifeki da ranar da aka kasheki da ranar da za a tasheki rayayya.
0 Comments