Yau Alhamis 1ga watan Muharram wanda yayi dai dai da 20/8/2020 yan uwa Almajiran Sayyed zakzaky (H) na dairan Kaduna suka fara gabatar da zaman Makokin Aba Abdullah imam Hussain domin tunawa da musibar data faru dashi a wannan watan na kisan Gilla babban Bako wanda ya gabatar da jawabi akan Falalan yin zaman Makokin Aba Abdullah imam Hussain (AS) shine Mal Aminu Badiko mal ya kawo Hadisai masu yawan gsky akan yin kuka sabida imam Hussain inda ya fara da Falalan karanta suruatul Ahad daganan mal ya cigaba da kawo Hadisi na imam Jafar ya kasan yana cewa duk wanda zaiyi kuka akan wani musibar da yafaru toh yayi kuka akan abinda ya faru da Aba Abdullah imam Hussain(as) daga qarshe Mal Aminu yayi kira ga Matasa da su zama samfuri ma'abota Addini ta wajan dabi'a da shiga sabida Matasa sune manyan Gobe a dukkan wani alamari na Addini inda daga qarshe wakilin yan uwa na Kaduna Mal Aliyu Turmizi yayi Ta"aliki daga karshe yayi kira ga yan uwa su rinqa zuwa akan lokaci kamar yanda aka saba sannan da takunkumi domin kaucewa daga kamuwar cutar corona
Ga wasu daga cikin hotunan da muka dauko muku a wajan
Kaduna Press
20/8/2020






0 Comments