Sharif wanda shine shugaban kwamitin amintattu na Coalition of Northern Groups (CNG) na hannun hedkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, jaridar Tribune Online ta ruwaito.
A wata takardar da Tribune Online ta samu daga CNG wacce kakakin kungiyar, Abdulazeez Suleiman yasa hannu, ta ce an kama Sharif bayan sun kammala zanga-zangar da suka yi a Katsina a ranar Talata.
Idan zamu tuna, a ranar Talata, dubban matasa daga jihohin arewa karkashin inuwar CNG suka hadu a Katsina inda suka yi zanga-zanga a kan ta’azzar ayyukan ‘yan bindiga a yankin.
Wannan ce babbar zanga-zanga ta farko da ta tattara matasa daga kungiyoyi masu tarin yawa.
A baya mun kawo maku cewa dandazon jama’a a jihar Katsina sun fito domin yin zanga-zanga a kan hauhawan rashin tsaro a fadin jihar.
Masu zanga-zangar sun kawar da shingen da jami’an yan sanda suka sanya a manyan tituna yayin gudanar da tattakin nasu.
A wani sakon murya da majiyar mu ta samu, an jiyo daya daga cikin jagororin zanga-zangar mai suna Kwamrad Usman Hussaini Rafuka yana fadin cewa:
“Musababbin wannan zanga-zangar da muka shirya, kowa dai ya sani musamman indai mutum yana a yankin arewacin Najeriya, ya san menene musababbin.
“Musababbinta bai wuce yanayin yadda ake kisan al’umma, musamman idan aka dauki jihar Katsina, muna da kananan hukumomi kusan 15 wanda a kullun sai an zub da jini a wannan yankin.
“Da wuya ka ji an ce ba a kashe mutum 20 ba kai har mutum 100 ana kashewa a rana daya.
“Yanzu haka maganar da nake yi da safe akwai wanda yana daga cikin masu wannan zanga-zangar lumanan da muka shirya, wanda da safen nan na kira shi ya batun tafiya sai yake ce mun wallahi yanzu haka a jiya a Batsari akwai wani gari an shiga an tafi da kanin mahaifinsa.
“Wannan ne dalilin da yasa ma ba zai samu halartan zanga-zangar ba. Kin ga kenan shi abun dake faruwa a jihar ya ma shafe shi.”

0 Comments