Cibiyar tallafa wa yaran shahidan Zariya ta shirya wani taron manema labarai a safiyar yau Lahadi 8 ga watan Disamba 2019, a birnin Tehran, wanda 'yar Sheikh Ibrahim Al Zakzaky cewa da Suhaila ta halarta.
Yayin taron ta yi tuni da kisan killan da sojoji sukayi wa almajiran Shehun Malamin a ranar 12 ga watan Disamba 2015.
Taron na cika shekaru hudu da harin da sojojin na Najeriya karkashin jagorancin babban hafsan sojin Najeriya Tukur Burutai suka kai a Zariya.
Yayin taron Malama Suhaila ta bayyana cewa matakin da kotu ta dauka na baya bayan nan ya basu matukar tsoro saboda barazana ce lafiyar iyayensu.

0 Comments